Shugaban kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya bayyana a ranar Litinin cewa, kungiyar NATO za ta kaddamar da wata tawagar da ba ta yaki ba a kasar Afghanistan tun daga ranar daya ga watan Janairun shekarar 2015. Tawagar mai taken "Resolute Support" wato tallafin da ya dace na da manufar ba da horo, shawara da ba da taimako ga jami'an tsaron kasar Afghanistan, in ji mista Stoltenberg. Hakan ya nuna nasarorin da aka samu cikin hadin gwiwa bayan an sadaukar da rayuka, amma wannan zai taimaka wa gina Afghanistan bisa nasarorin da aka samu, in ji shugaban na NATO. (Maman Ada)