A kasar Saliyo, cibiyar kasa da ke yaki da cutar Ebola (NERC) ta tabbatar wa kafofin watsa labarai cewa, shirin nan na yaki da cutar Ebola wato "Operation Northern Push" zai ci gaba, har sai an ga cewa babu mai dauke da cutar Ebola a yankunan kasar da ke fama da wannan cuta.
Manjo Pallo Conteh, babban darektan NERC, a lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida bayan ziyararsa a wadannan yankunan da ke fama da Ebola a ranar Laraba da yamma, ya bayyana cewa, matakin dokar hana fita da aka sanya a yankunan Port Loko da Kambia, da ya kare a ranar Talata, za a sake mai da shi a cikin yankunan biyu, amma duk da haka ya nuna cewa, za a iya sake duba wannan mataki idan aka samu wasu sauye sauye.
A cewar mista Conteh, kowa ne daga cikin yankunan da cutar ta fi kamari, za su samu kayayyaki da shawarwarin da suke bukata domin ganin babu mai dauke da wannan cuta.
Haka kuma ya shaida wa kafofin watsa labarai cewa, ya samu kwarin gwiwa kan yadda aka kula da gidajen da aka kebance duk da matsalolin kayayyakin aiki da aka fuskanta, tare da nuna cewa, abinci, magunguna da kayayyakin tsimi, an kai su cikin lokaci, kana kuma jami'an tsaro sun tsare gidajen da aka kebance, da kuma shingayen da aka kafa, an tanadar masu kayayyakin aiki yadda ya kamata.
Mista Conteh ya bayyana cewa, al'ummomi sun fara fahimta cewa, suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen sanya ido, da kuma tallafawa gidajen da aka kebance dalilin cutar Ebola. (Maman Ada)