in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon zai jagoranci taron farfadowa daga Ebola
2015-07-07 09:58:58 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, zai jagoranci wani taron karawa juna sani game da farfadowar kasashe daga cutar Ebola, taron da ake sa ran gudanar sa a birnin New York a ranar Juma'a.

A cewar mataimakin mai magana da yawun MDD Farhan Haq, taron zai gudana ne da hadin gwiwar kungiyar hadin kan Afirka AU, da takwararta ta Turai EU, da bankin duniya tare da bankin raya Afirka. Kaza lika Mr. Haq ya ce, tuni shuwagabannin kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo suka nuna aniyar su ta goyon bayan taron.

Makasudin taron dai shi ne tabbatar da ganin cewa, kasashen da cutar Ebola ta shafa sun samu tallafin da ya dace. Hakan kuwa na zuwa ne a gabar da ake samun sabbin masu harbuwa da cutar ta Ebola a Liberia, lamarin da masu ruwa da tsaki ke ganin ba wani abun mamaki ba ne, ganin cewa tuni masana suka yi kashedin aukuwar hakan.

Wani rahoto na hukumar lafiya ta duniya ko WHO ya nuna cewa, a farkon watan Yunin da ya shude, an samu sabbin wadanda Ebola ta kama har mutane 31, a wasu yankunan kasashen Guinea da Saliyo. Kana a sati na biyu na watan kuma aka samu karin mutane 14 da suka harbu.

Alkaluman baya bayan nan sun shaida karuwar sabbin mutane da Ebola ke kamawa cikin makwannin biyu a jere.

A baya dai kasar Sin, da kungiyar tarayyar Turai da kuma MDD, sun baiwa kasashen yammacin Afirka uku da cutar ta fi kamari tallafi na dakile yaduwar ta, yayin da hankulan al'ummar duniya ke karkata ga barazanar da cutar ke yiwa rayuwar bil'adama. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China