in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana shirin kota-kwana bayan da Ebola da sake bullo a Liberia
2015-07-03 09:25:30 cri

Gwamnatin Najeriya ta fargad da al'ummar kasar da su kasance cikin shirin kota-kwana, kana su kasance masu kula da tsafta bayan da cutar Ebola da sake bulla a kasar Liberia.

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta tarayyar kasar Ayotunde Adesugba ya bayyana cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai cewa, ma'aikatar ta sake farfado da matakan kandagarki da na fadakar da jama'a game da cutar.

Don haka ya bukaci gwamnatocin jihohin kasar da su ma su kara ilimantar da jama'a game da cutar, sannan su mikawa ma'aikatar lafiya ta tarayya duk wani mutum da ake zaton ya kamu da cutar.

Babbar sakatariya a ma'aikatar lafiyar kasar Modele Osunkiyesi ta ce, wannan mataki da mahukuntan kasar suka dauka ya zama wajibi ganin yadda cutar da sake bullo da kasashen Liberia da Saliyo da ke makwabtaka da kasar ta Najeriya.

Yanzu haka ma'aikatar lafiya ta tarayya da takwarorinta na jihohin kasar da sauran masu ruwa da tsaki na sa-ido sosai don ganin ba a samu bullar cutar a kasar ba.

A ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2014 ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana Najeriya a matsayin kasar da ta kawar da cutar Ebola a cikin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China