Hukumomin kasar Guinea na gudanar tun daga ranar Talata da wani aikin killace wasu garuruwan da ke fama da cutar Ebola a yankin Basse Guinea. A cikin gundumar Boke, mai tarazar kilomita 100 da Conakry, hedkwatar kasar, an tabbatar da harbuwar mutane goma sha daya a ranar Alhamis, daga cikinsu mutane shida sun mutu, a cewar wasu majiyoyi masu tushe.
Garurura takwas ne aka killace a gundumomin Dubreka mai nisan kilomita 50 da birnin Conakry, da kuma Forecariah mai nisan kilomita 100 da birnin Conakry.
Wannan aiki na da nufin takaita zirga zirgar mutane. Al'ummomin wadannan yankuna da abin ya shafa za su kwashe 21 wuri daya. (Maman Ada)