A jiya ne a nan birnin Beijing Yu Zhengsheng, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC ya gana da tawagar jam'iyyar ZANU-PF ta kasar Zimbabwe, karkashin shugabancin mataimakin shugaban jam'iyyar kana mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa.
A yayin ganawar, mista Yu ya ce, shekarar bana, shekara ce ta cikon shekaru 35 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe. Kasar Sin na fatan inganta hadin gwiwa da Zimbabwe, a kokarin raya dangantakar da ke tsakaninsu zuwa abin misali, wadanda suke amincewa da juna, yin zaman daidai wa daida, mara wa juna baya, da hada kansu domin samun moriyar juna da bunkasuwa tare.
A nasa bangaren, mista Mnangagwa ya ce, kasarsa na fatan inganta hadin gwiwa da Sin ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. (Tasallah Yuan)