in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta baiwa Zimbabwe rancen kudi don kyautata aikin samar da wutar lantarki
2013-11-12 10:50:45 cri
Ran 11 ga wata, bankin shige da ficen kasar ta Sin, da hukumar kula da harkokin kudi ta kasar Zimbabwe, sun sa hannu kan wata yarjejeniya, cewa bankin na Sin zai ba da rancen kudi har dallar Amurka miliyan 320 ga gwamnatin kasar Zimbabwe, don gudanar da aikin habaka tashar samar da wutar lantarki, mai amfani da ruwa da ke kudancin Kariba.

Tashar samar da wutar lantarkin ta kudancin Kariba, ita ce tasha mafi girma a kasar, sai dai rashin isashen injunan samar da wutar lantarkin, ya sanya ta samun koma baya, lamarin da ya haifar da tarnaki ga ayyukan samar da wutar lantarki a kasar.

An dai hakikance cewa, karancin wutar lantarki a kasar tsahon shekaru, ya tilasawa Zimbabwen sayan wutar lantarki daga kasashe makwabtanta, wanda hakan ke haifar da kalubale ga aikin farfado da tattalin arzikin ta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China