A yayin ganawar da suka yi a jiya Laraba, Guo Jinlong ya yabawa shugaba Mugabe, da kasancewarsa jagora dake matukar kokarin kasarsa ta samu cikakken 'yanci a nahiyar Afirka, baya ga gudummawar da ya bayar wajen samun 'yancin kai da ci gaba a nahiyar Afirka, da raya dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, da ma dangantakar daukacin kasashen Afirka da kasar ta Sin.
Mr. Guo ya ce bayan kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasarsa da Zimbabwe, yanzu hakan ana inganta wannan dangantaka yadda ya kamata. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da bi ka'idojin sada zumunta da na hadin gwiwa, wajen raya dangantakar aminci a tsakaninta da kasashen Afirka, ciki har da kasar Zimbabwe, bisa manufar hadin gwiwar Sin da Afirka da firaministan Sin Li Keqiang ya gabatarwa kungiyar AU a bana.
A nasa bangare, shugaba Mugabe ya bayyana cewa, kasarsa na godiya ga irin taimako da Sin ke ba ta wajen inganta tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, da kuma goyon baya gare ta kan harkokin kasa da kasa. Ya ce, Zimbabwe na dora muhimmanci kwarai ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da kuma dangantakar jam'iyyun kasashen biyu. Daga nan sai ya yi fatan kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da ayyukan more rayuwa, da sashen makamashi da dai sauransu, a kokarin daga darajar dangantakar sassan biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)