in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Zimbabwe sun yi shawarwari a tsakaninsu
2014-08-25 21:18:23 cri

Yau Litinin 25 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Zimbabwe Robert Mugabe a nan birnin Beijing.

A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya darajta danzon zumuncin da ke tsakanin kasashen 2 da kuma muhimmiyar gudummowar da shugaba Mugabe yake bayarwa wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen 2. Ya kuma jaddada cewa, jama'ar kasar Sin muna sa muhimmanci kan wannan zumunta. Har abada ba za mu manta da abokan arziki ba, wadanda suka dade suna raya abokantaka da mu, kuma muna mara wa juna baya, tare da kara fahimtar juna . Kasar Sin na son hada kai da kasar Zimbabwe wajen ci gaba da raya danzon zumuncin da ke tsakaninsu da inganta hadin gwiwa a sassa daban daban, a kokarin ci gaba da kasancewa tamkar abokan arziki kuma 'yan uwa da ke yin zaman daidai wa daida da juna, neman samun moriyar juna da bunkasuwa tare.

Har wa yau shugaba Xi ya nuna cewa, kasar Sin da kasashen Afirka, abokai ne da suka taba jure wahala tare, don haka har abada ba za su manta da juna ba. Tabbas kasar Sin za ta cika alkawarin da ta yi wa kasashen Afirka dangane da raya hulda a tsakanin bangarorin 2 bisa ka'idar nuna sahihanci ba tare da rufa-rufa ba, daukar hakikanin matakai, da raya dankon zumuncin da ke tsakaninsu. Zimbabwe za ta karbi shugabanci karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka a shekara mai zuwa, kasar Sin na son yin kokari tare da ita wajen raya huldar abokantaka ta sabon salo a tsakanin kasashen Sin da Afirka zuwa sabon mataki.

A nasa bangare kuma, shugaba Mugabe ya bayyana fatansa na inganta hadin gwiwa da kasar Sin, a kokarin ci gaba da bunkasa huldar da ke tsakanin kasarsa da Sin. Zimbabwe ta gode wa kasar Sin bisa nuna adalci a cikin al'amuran kasa da kasa, tare kuma da nuna wa kasashen Afirka girmamawa, tana yin zaman daidai wa daida da kasashen Afirka, tare da taimaka musu wajen tsayawa da kafarsu. Kasarsa ta Zimbabwe na son hada kai da kasar Sin wajen kyautata bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasashen Afirka da Sin. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China