in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da shugaban Zimbabwe
2014-08-26 21:02:28 cri

Yau Talata 26 ga wata, a nan birnin Beijing, Zhang Dejiang, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe na kasar Zimbabwe, wanda ke ziyara a nan kasar Sina nan Beijing.

A yayin ganawarsu, Zhang Dejiang ya darajta gudummowar da shugaba Mugabe ya bayar wajen samun 'yancin kai da bunkasuwar kasar ta Zimbabwe da kuma sha'anin 'yantar da al'ummar Afirka. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na son hada kai da Zimbabwe wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen 2 suka cimma daga dukkan fannoni, tare da zurfafa hadin gwiwar neman samun moriyar juna, a kokarin kara jawo wa jama'ar kasashen 2 alheri.

A nasa bangare kuma, shugaba Mugabe ya ce, kasarsa ta Zimbabwe ta darajta dankon zumuncin da ke tsakaninta da Sin, ta gode wa kasar Sin bisa goyon baya da taimakon da take ba ta. Yana fatan kara zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China