A shekarar 2012 ne dai Mohammed Morsi ya dare karagar mulkin kasar ta Masar, a matsayin shugaba na farko farar hula da jama'ar kasar suka zaba. Sai dai daga bisani sojojin kasar sun hambarar da shi daga shugabancin kasar cikin watan Yulin shekarar 2013.
Haka kuma, hukumar gabarar da kararraki ta kasar ta taba bayyana cewa, manyan jami'an kungiyar 'yan uwan Musulmi, cikin hada da Mohammed Morsi, da kuma wasu mambobin kungiyar Hamas ta Falesdinu, da 'yan kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, da kuma wasu mambobin kungiyoyin masu aikata laifuffuka, sun shirya fasa gidan yarin kasar a ranar 28 ga watan Janairun shekarar 2011. (Maryam)