in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kwamitin NPC ya halarci bikin rufe taro karo na 15 na zaunannen kwamitin NPC na 12
2015-07-01 20:16:40 cri
Shugaban kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) Zhang Dejiang, ya halarci bikin rufe taro karo na 15, na zaunannen kwamitin NPC na 12 da sanyin safiyar Larabar nan, inda ya gabatar da jawabin sa bayan zartas da kudurori a taron.

Zhang Dejiang ya ce, a yayin wannan taro, an yi nazari da kuma zartas da dokar tsaron kasa, dokar da za ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye tsaron kasa, da tabbatar da babbar moriyar jama'a.

Bayan haka, Zhang ya ce, an zartas da kudurin yin rantsuwa bisa tsarin mulkin kasa a gun taron, wato bisa sabuwar dokar, shugabannin kasar za su gudanar da rantsuwa bisa tsarin mulki a yayin da za su kama aiki a mukamansu. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China