in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban NPC ya tattauna da takwaransa na Kenya kan karfafa dangantaka
2015-05-18 21:20:51 cri

Shugabannin majalissar dokokin kasar Sin da na kasar Kenya a ranar litinin din nan suka kara alkawarin karfafa dangantakar majalissun su a lokacin tattaunawa tsakanin Zhang Dejiang, shugaban majalissar wakilan jama'ar kasar Sin da shugaban majalissar dokokin kasar Kenya Justin Muturi, a zauren taron jama'a dake nan birnin Beijing.

A tattaunawar Zhang Dejiang wanda ya jaddada muhimmancin karfafa zumunci tsakanin sassan biyu, yayi kira ga majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin da majalissar wakailan na Kenya da su inganta fahimtar al'amurran kasashen juna ta yadda zasu samar da amincewar siyasa, fahimtar juna da kuma musayar a dukkan matakai domin shimfida tushen siyasa mai karfi wajen dangantakar zumunci.

A nashi bangaren Justin Muturi yace majalissar dokokin Kenya tana dora muhimmancin babba akan cigaba da zumunci da jam'iyar Kwaminis kuma a shirye take ta inganta hakan a dukkan matakai.

Haka kuma Yace majalissar dokokin Kenya tana son karfafa fahimtar juna da tabbatar da aminci sannan ta bada sabuwar gudunmuwa a wajen hadin gwiwwa a duk bangarori.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China