A safiyar yau jumma'a 5 ga wata ne Shugaba Xi ya bayyana haka lokacin da kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) suka kira taron murnar cika shekaru 60 da kafa NPC.
Shugaban na Sin yace a cikin sabon yanayin da ake ciki, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan demokuradiyya da tsarin NPC, tare da kyautata tsarin NPC yadda ya kamata, domin ci gaba da sa kaimi ga bunkasa tsarin siyasa iri na gurguzu.(Fatima)