Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilai karo na 11 ta kasar Sin Wu Bangguo, ya lashi takwabin ganin an mutunta doka da oda yayin tafiyar da harkokin mulki da inganta rayuwar jama'a ta hanyar sa-ido yadda ya kamata.
Mr. Wu ya bayyana cewa, "za mu yi kokarin ciyar da tsarin bin doka da oda gaba wajen tafiyar da harkokin kasa, karfafa muhimmancin irin rawar da doka ke takawa wajen tafiyar da harkokin kasa da inganta rayuwar jama'a".
Wu Bangguo ya bayyana hakan ne, yayin da yake gabatar da rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar wakilai karo na 11 a taron shekara-shekara na majalisar wakilan da ke gudana.
Wu ya ce zaunannen kwamitin zai yi kokarin karfafa sa-ido kan harkokin majalisar wakilai, kotun kolin kasar da kotun kolin sauraron kararraki, inda ya ce ta haka ne za a mutunta doka tare da yin aiki da ita wajen hukunta wadanda suka keta doka.
Bayan nazarin aikin na shekaru biyar da suka gabata, Wu ya yi alkawarin hanzarta gina kasa mai bin tsarin gurguzu bisa doka da oda, tare da sanya dukkan ayyukan kasar bisa tafarkin doka.
Ya kuma bayyana cewa, za a kara ilimantar da jama'a game da doka, ta yadda za su bayyana bukatunsu, kare 'yanci da muradunsu, da kuma sasanta rikice-rikice, har ma tsakanin jami'an gwamnati. (Ibrahim)