Bisa goron gayyatar shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark da kuma shugaban majalisar wakilan kasar Aminu Tambuwal, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya kai ziyarar sada zumunta a hukunce a kasar Najeriya tun daga ranar 17 zuwa 19 ga wata. A yayin ziyarar tasa ya gana da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan,tare da yin shawarwari da shugaban majalisar dattawa David Mark, da shugaban majalisar wakilai Aminu Tambuwal, ya kuma gana da shugaban jam'iyyar PDP Bamanga Tukur a Abuja babban birnin Najeriya.
A yayin ziyararsa a kasar ta Najeriya, Zhang Dejiang ya halarci jerin bukukuwan "kara fahimtar al'adun Sinawa" da kuma bude cibiyar al'adun kasar Sin a tarayyar Najeriya. Bugu da kari, mista Dejiang ya kuma halarci bikin kara fahimtar kasar Sin, inda aka mika "cibiyar Sin" ga babban dakin karatu na Najeriya. ya kuma kai wani rangadi zuwa ofishin kula da harkokin tsaron intanet na kasar Najeria da kamfanin sadarwa na Zhongxing na Sin ya gina. (Maryam)