in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kwaskwarima ga dokar kasar Sin da ke baiwa al'umma damar kai gwamnati kara
2014-11-01 21:03:10 cri
Mambobin babban kwamitin majalissar wakilan al'ummar duk kasa ta NPC, sun amince da yi wa dokar da ta tanaji baiwa al'ummar kasar Sin damar gurfanar da gwamnati gaban kuliya gyaran fuska.

Kwaskwarimar da aka yiwa wannan doka dai na da nufin baiwa Sinawa karin dama, idan har akwai bukatar su shigar da gwamnatin kasar kara.

Kafin amincewa da gyaran fuskar dai sai da aka kada kuri'a, gabanin kammalar zaman majalissar na mako guda.

Wakilan majalissar ta NPC dai sun bayyana daukar wannan mataki a matsayin wani kuduri da ya yi daidai da dokokin kasar, da ma bukatun al'umma.

Sakamakon hakan kotu na da ikon fara bincike kan batutuwan da suka shafi karar da al'ummar kasar ta Sin za su shigar tsakanin su da gwamnati, kan sha'anin mallakar filaye, da muhallai, da batun biyan diyya, da ma wasu harkokin cinikayya.

Kaza lika sauyin ya tanaji umartar gwamnati ta yi biyayya ga dokokin da suka jibanci wadannan sassa, ko ta biya idan har aka tabbatar an sabawa dokokin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China