A yayin bikin da aka yi a birnin San Francisco, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, MDD ta kasance alama ta fata ga duk duniya,kuma gidan al'ummomin kasa da kasa. Kudin tsarin MDD shi ne babbar manufar MDD, dake bada jagoranci ga al'ummomin kasa da kasa na ganin sun dukufa domin neman makoma mai kyau.
Haka kuma, a yayin bikin da aka yi a hedkwatar MDD dake birnin New York, mataimakin zaunannen babban magatakarda Jan Eliasson ya ce, tushen kundin tsarin MDD shi ne bayyana fatan su, kuma an kafa kundin ne a lokacin da aka kawo karshen yanayi mafi tsanani cikin tarihin dan Adam, don haka, kundin ya dauki nauyin buri da kuma fatan al'ummomin duniya sama da biliyan 7.
A ran 25 ga watan Yuni na shekarar 1945, wakilan da suka zo daga kasashen 50 da suka fafata a yakin duniya na biyu sun zartas da kundin tsarin MDD baki daya a yayin taron kafa tsarin mulki da aka yi a birnin San Francisco, sai kuma a ranar 26 suka sa hannu kan kundin, inda aka bude hanya wajen kafa MDD. (Maryam)