in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ba da lambobin yabo ga sojoji 558 na kasar Sin a kasar Liberia
2015-06-04 19:13:17 cri
A yau Alhamis 4 ga wata, aka yi bikin bada lambobin yabo ga tawaga ta rukuni na 17 ta na sojojin Sin masu kiyaye zaman lafiya dake kasar Liberia a sansanin rukunin sojoji ma'aikata na birnin Zwedru dake kudu maso gabashin kasar, inda aka bada lambobin yabo na kiyaye zaman lafiya na MDD ga sojoji 558 na kasar Sin.

Wakiliyar musamman na babban sakataren MDD Karine Landgren da manyan jami'an tawagar musamman ta MDD dake kasar Liberia da hafsoshin tawagogin rundunonin kasa da kasa masu kiyaye zaman lafiya dake kasar Liberia da jami'an gwamnatin jihar Grand Gedeh fiye da 150 suka halarci bikin.

Madam Karine Landgren a jawabin ta wajen bikin ta yabawa sojojin Sin masu kiyaye zaman lafiya tana mai cewa, sojojin na kasar Sin sun yi kokarin gudanar da ayyuka ba tare da yin la'akari da kansu ba, sun bada gudummawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da yaki da cutar Ebola a kasar Liberia, kuma su ne abin koyi ga dukkan sojojin kiyaye zaman lafiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China