Wang Min ya nuna cewa, da farko dai, ya kamata kasashen duniya su kafa tunanin kasancewarsu tamkar cikin kungiya daya ta cimma buri daya na bunkasa yankunan teku tare, da yakar kalubale cikin hadin gwiwa, da su bada karin hadin gwiwa irin na a zo a gani domin cimma burin samun ci gaba tare. Sannan su kara yin hadin gwiwa wajen daidaita al'amura, ta yadda za a iya cimma burin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma da kiyaye ingancin muhalli tare. Bugu da kari, ya kamata a kara karfin kasashe masu tasowa, ta yadda za a iya tabbatar da ganin dukkan kasashen duniya sun samu ikon kafa ajanda da ka'idoji na kasa da kasa cikin zaman daidai wa daida. Ya kamata kasashen duniya su fi mai da hankali wajen daidaita matsalar yadda za a iya kara karfin kasashe masu tasowa da kuma tabbatar da ganin sun samu daidaitaccen iko a yankunan teku.
Wang Min ya kara da cewa, bangaren Sin na fatan kara yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya domin ba da karin gudummawa ga kokarin bunkasa yankunan teku. (Sanusi Chen)