A Jiya Litinin ne dai kwamitin binciken ya sanar da cewa, bisa sakwanni da bayanan da aka samu, akwai yuwuwar cewa dukkan sassan biyu sun aikata laifukan yaki, a rikicin na zirin Gaza wanda aka shafe tsawon kwanaki 51 ana kwabzawa. Rahoton ya yi nuni da cewa, rikicin ya fi yin barna ga zirin Gaza da ma al'ummar sa.
Palesdinawa fiye da 2100, da yahudawan Isra'ila fiye da 70 ne suka rasu a sakamakon rikicin. A daya hannun rahoton ya yi Allah wadai da kazawar gazawar da aka yi wajen dakile hare-haren soja da Isra'ila ta kaddamar, musamman a lokutan da ta san hare-haren zasu haifar da illar gaske ga fararen hula masu yawa.
Hakazalika kuma, rahoton ya yi tir da hare-haren roka kan yankunan Isra'ila, wadanda dakarun zirin Gaza suka aiwatar, ba tare da yin la'akari da fararen hula ba. (Zainab)