Kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da taron shekara-shekara na hafsoshin da ke jagorantar ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a wannan rana, inda Wang Min ya bayyana cewa, domin dacewa da sauyawar yanayin jibge rundunonin musamman na MDD masu kiyaye zaman lafiya da kuma umarnin da aka ba su, ya kamata a kara daidaita ka'idojin musayar wuta, da takardun bayani ga kasashen da za su tura sojojin kiyaye zaman lafiya, a kokarin aiwatar da muhimman ka'idojin ayyukan kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata.
Wang Min ya kara da cewa, an kammala aikin jibge sojojin kasa na Sin dake aiki a laimar tawagar MDD ta musamman dake kasar Sudan ta Kudu, kuma wannan ne karo na farko da Sin ta tura sojojin kasa don shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. Kana Sin ta tsaida kudurin tura rukunin jiragen saman masu saukar ungulu ga tawagar MDD da kungiyar AU ta musamman dake yankin Darfur, shi ma wannan zai zama karo na farko da Sin ta tura sojojin sama ga tawagar.
Hakazalika kuma, Wang Min ya ce, Sin za ta ci gaba da mara wa kasashen Afirka baya wajen inganta karfin kiyaye zaman lafiya, da sa kaimi ga MDD da ta kara nuna goyon baya ga kungiyar AU da sauran kungiyoyin yankuna wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya. (Zainab)