in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya kalubalanci Amurka da kasashen Turai da su dubi kansu game da batun kare hakkin dan Adam
2015-06-25 10:56:34 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Genevan kasar Switzerland Wu Hailong, ya zargi kasar Amurka, da kungiyar EU, da kasar Jamus, da wasu sauran kasashen dake ci gaba da nuna yatsa ga kasar Sin, da makamantan ta, kan batun kare hakkin dan Adam ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Duk kuwa da cewa ana samun matsalolin keta hakkokin bil'adama a Amurkan, da ma kasashen na Turai.

Game da hakan Mr. Wu ya ce ya dace wadannan kasashen su fara duban kan su tukuna, kafin su soki sauran kasashe. Mr. Wu wanda ya bayyana hakan yayin taro na 29, na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD da ya gudana a jiya Laraba, ya kara da cewa an shafe tsahon lokaci ana keta hakkin 'yan asalin Afirka mazauna Amurka, kuma rikicin kabilanci na tsananta, yayin da ake ci gaba da nuna wariya ga bakaken fatar kasar a fannonin samun guraben ayyukan yi, da muhalli, da ilimi, baya ga banbanci da 'yan sanda ke nunawa bakaken fatar yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Game da wannan batu a kasashen Turai kuwa, Wu Hailong ya bayyana cewa, matsalar nuna wariyar launin fata da kabilanci ga 'yan kasashen waje, da kyamar addinai na kara tsananta a kasashen Turai da dama, ciki har da rashin bada kariya ga musulman kasashen waje dake zaune a sassan wadannan kasashe.

Mr. Wu ya jaddada cewa, Sin na kara kira ga bangarori daban daban da su rungumi tsarin mulkin MDD, da ka'idojin gudanar da ayyuka da aka tabbatar da su cikin kuduri mai lamba 60 da lamba 251 na MDD, su kuma yi watsi da ayyukan nuna kiyayya da matsin lamba, tare da warware matsaloli ta hanyar shawarwari da hadin gwiwa, da sa kaimi ga inganta sha'anin tabbatar da hakkin dan Adam na kasa da kasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China