Professor Li Daojun na cibiyar nazarin kare hakkin dan Adam ta jami'ar Shandong ya yi bayani a cikin sharhinsa cewa,tun bayan da aka bude kofa da yin kwaskwarima a cikin gida, Sin ta bullo da wata hanya musamman ta tabbatar da kare hakkin dan Adam, da shigar da tabbatar da ganin an girmama batun kare hakkin dan Adam a cikin kundin tsarin mulkin kasar, wannan tsarin ya taimaka wajen tabbatar da ganin ana kare hakkin dan Adam a kasar. A gun cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya karo na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an gabatar da shirin gudanar da harkokin kasa bisa dokoki daga manyan fannoni a dogon lokaci. Ta haka Sin ta riga ta bude kofar yin kwaskwarima da kirkire-kirkire kan tsarin shari'a bisa tushen tabbatar da kare hakkin dan Adam. Sharhin ya ce, kungiyar sa ido kan kare hakkin dan Adam ta raina nasarorin da kasar Sin ta samu wajen tabbatar da kare hakkin dan Adam, da kuma kokarin da Sin ta yi wajen yin kwaskwarima don tabbatar da ganin ana kare hakkin dan Adam. Kungiyar ta juya baya ga abubuwa na zahiri, inda ta bayyana abubuwa marasa tushe.
Mataimakin farfesa a cibiyar nazarin kare hakkin dan Adam ta jami'ar ilmin siyasa da dokoki ta Southwest ta kasar Sin Meng Qingtao ya yi bayani a cikin sharhinsa cewa, wata kasa ba ta da ikon yin magana game da hakikanin yanayin kare hakkin dan Adam na wata kasa daban. Muddin ba a ji daga bakin jama'ar kasar ba,duk wani rahoton game da kare hakkin dan Adam da za a wallafa, rahoto ne da ba shi da tushe ko kadan. (Zainab)