Mr. Wang ya bayyana hakan ne yayin zaman babban kwamitin majalisar MDD wanda ya maida hankali, ga gudanar da muhawara kan batun kare hakkin dan Adam, inda ya ce kasar Sin tana fatan ganin ta kara kaimi ga samun bunkasuwa tare da ragowar sassan duniya baki daya. Kuma samun ikon rayuwa da ikon samun bunkasuwa shi ne kan gaba ga kasashe masu tasowa da za su gudanar a fannin kare hakkin dan Adam.
Ban da wannan kuma, Wang Min ya ce, sha'anin kare hakkin dan Adam muhimmin kashi ne na inganta tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasar Sin. Ya ce a kokarinta, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa mai alamar kasar Sin kan kare hakkin dan Adam, matakin da ya tabbatar da ikon bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma da al'adunsu, dama na hakkin jama'ar da kuma na ikon siyasa. (Zainab)