in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya gabatar da ra'ayoyi 4 dangane da yadda ake kiyaye hakkokin dan Adam a duniya
2015-03-05 20:41:07 cri

A yau ne jakada Fu Cong, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa da ke Geneva na kasar Switzerland ya yi jawabi a babbar muhawarar da aka shirya a babban taro karo na 28 na kwamitin kula da hakkokin dan Adam na MDD, inda ya yi bayani kan yadda kasar Sin take raya sha'anin kiyaye hakkokin dan Adam, tare da gabatar da ra'ayin kasar ta Sin kan raya wannan sha'ani a duniya.

A jawabinsa, Fu Cong ya ce, da farko dai dole ne a sake nanata alkawarin da aka yi dangane da kundin tsarin MDD, a tsaya tsayin daka kan bin ka'idojin rashin nuna wani bambanci ga ikon mulkin kasa da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, a kokarin kara azama kan raya huldar da ke tsakanin kasa da kasa ta hanyar dimokuradiyya bisa dokoki. Na biyu, dole ne a girmama mabambantan halin da kasashen duniya suke ciki a fannin raya hakkokin dan Adam. Tilas ne a girmama al'adun gargajiyar ko wace kasa da tunaninta, da tsarin zaman al'ummarta, hanyar raya kasa da kuma hanyar kiyaye hakkokin dan Adam da ta zaba da kanta. Na uku kuma dole ne a daidaita hakkokin dan Adam cikin adalci, musamman ma hakkin al'ummomin kasashe masu tasowa a fannonin rayuwa a duniya da samun bunkasuwa. Kamata ya yi a ba da muhimmanci ga batun kawar da talauci da sa kaimi kan ci gaba a cikin shirin bunkasuwa bayan shekarar 2015. Na hudu kuwa, tilas ne a daidaita sabani yadda ya kamata ta hanyoyin yin tattaunawa da hadin gwiwa. Kamata ya yi tun farko a yi zaman daidai wa daida da girmamawa juna, ta yadda kasashen duniya za su yi koyi da juna, sannan su kauce wa matsawa juna lamba da nuna adawa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China