in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi suka game da yanayin kare hakkin dan Adam na kasar Amurka
2015-05-14 15:10:38 cri

A 'yan kwanakin baya, wasu kwararru da kafofin watsa labaru na kasashen Rasha, da Malaysia, da Masar, da Kenya, da kuma Sham da kungiyoyin kasa da kasa sun fidda sharhi kan yanayin kare hakkin dan Adam a kasar Amurka.

Da dama daga masharhantan dai sun yi suka ga yanayin kare hakkin dan Adam a kasar ta Amurka, yayin da kasar ke fuskantar manyan matsaloli a fannoni da dama, ciki har da daukar matakai masu tsanani wajen gudanar da shari'u, da nuna bambancin launin fata da 'yan sandan kasar ke yi, da tsaurara yanke hukunci, da sa ido da hukumomin liken asirin kasar suke yi. Masharhantan dai sun bayyana bukatar kasar na kawo karshen wadannan batutuwa da suka shafi hakkin dan Adam.

Hukumar kula da kare hakkin dan Adam ta MDD ta tantance yanayin hakkin dan Adam na kasar Amurka da ake fitarwa lokaci bayan lokaci, a ranar 11 ga wannan wata da muke ciki a birnin Geneva na kasar Switzerland. A wannan lokaci ne kuma wakilan kasashe kimanin 120 suka ba da jawabi a gun taron game da yanayin hakkin dan Adam a kasar Amurka, ciki har da amfani da karfin da ya wuce kima da 'yan sanda ke yi, da nuna bambancin launin fata da 'yan sandan kasar ke nunawa da dai sauransu.

Tantance yanayin hakkin dan Adam lokaci bayan lokaci, wani tsari ne da hukumar kula da hakkin dan Adam ta MDD ta tsara, da nufin binciken yadda kasashe daban daban suke aiwatar da alkawaran su game da kare hakkin bil Adama. An kuma fara gudanar da tsarin ne tun daga shekarar 2008, inda ake tantance dukkan kasashen duniya bayan kowane shekaru 4. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China