Kakakin hukumar George Little a wata sanarwar da ya fitar ya ce yana da tabbacin cewa sojojin Amurka ne suka kai wannan samame cikin dare ga maboyar kungiyar a ranar Jumma'a, sai dai bai bayyana tsarin da suka bi ba da kuma wadanda harin ya shafa ba.
Kafar yada labarai na kasar Amurka tun da farko sun sanar da cewa wani babban jami'in kasar ya ce rundunar sojojin ruwa na SEAL suna cikin wadanda suka kai samamen ma kungiyar dake da sansani a Somaliya. Sai dai ya ce sojojin Amurkan sun janye kafin su tabbatar da ko sun samu kashe wadanda suke son yi domin su ma an mai da masu martani ta hanyar bude masu wuta, sai dai babu sojan rundunar ta SEAL da wannan martani ya shafa, in ji jami'in.
Gidan Radiyon kasar Somaliya da mazauna a ranar Asabar sun bayyana cewa wassu rundunar tsaron na kasashen waje da ba'a tabbatar da kasar su ba sun kai samame a wani gida da ya zama maboyar kungiyar dake garin Barawe a kudancin kasar a daren Jumma'a.
Harin da aka kai shi ta hanyar ruwa a wannan gidan da 'yan kungiyar ke tsare da shi, an dauki lokaci mai tsawo ana musanyar wuta tsakanin rundunar sojin da kungiyar, a cewar wani mazauni garin na Barawe a yankin Shabelle. (Fatimah Jibril)