Babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga manyan hukumomin kasa da kasa da su yi kokarin zuba jari a bangaren shirye-shiryen more rayuwar jama'a a kasar Somaliya, ta yadda za a samu saukin komawar 'yan gudun hijira zuwa kasar.
Mr Guterres ya shaidawa manema labarai a Nairobin kasar Kenya cewa, samun saukin mayar da 'yan gudun hijirar ya dogara ne ga yadda aka inganta harkokin tsaro da yanayin wurin da za su zauna.
Jami'in na MDD ya kuma ce, ya samu tabbaci daga shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta cewa, gwamnatinsa ba za ta tilastawa 'yan gudun hijirar Somaliya barin sansanin Dadaab ba, ko da yake a baya mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce, gwamnatin kasar ta ba da wa'adin watanni uku da a canza wa 'yan gudun hijirar Somaliya da ke zaune a sansanin na Dadaab matsuguni, saboda sansanonin na zama wuraren kyankyasar ta'addanci.
Ya kuma bayyana cewa, binciken tsaron da aka gudanar a yankunan ya nuna cewa, kamata ya yi a sake tsugunar da 'yan gudun hijirar, ta yadda za su bayar da gudummawa wajen sake gina kasashensu.
Nan ba da dadewa ba ne ake sa ran kiran wani taron kasa da kasa don tattauna hanyoyin samun kudaden da za a kwashe 'yan gudun hijirar Somaliya da ke zaune a irin wadanan sansanoni. (Ibrahim)