in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Kenya sun bayyana shirin mayar da 'yan gudun hijirar Somaliya gida
2015-06-12 09:40:15 cri

A jiya ne gwamnatin kasar Kenya da wasu abokan hulda suka bayyana shirinsu na kwashe 'yan gudun hijirar kasar Somaliya 100,000 da suke son barin sansanin da suke zaune don radin kansu nan zuwa watan Disamba.

Mai rikon mukamin kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun hijira Harun Komen wanda ya bayyana hakan ya ce, a mako mai zuwa ne ake sa ran fara shirin wanda ya dan samu tsaiko a baya sakamakon ruwan sama da a kai ta tafkawa kamar da bakin kwarya.

Da yake bayani a wani taron bainar jama'a da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya gabanin ranar 'yan gudun hijira ta duniya wato 20 ga watan Yuni, Komen ya nanata kudurin gwamnatin Kenya na martaba dokokin kasa da kasa a lokacin kwashe 'yan gudun hijiran na Somaliya.

Ya kuma ce, gwamnatin Kenya ba za ta mayar da 'yan gudun hijirar da karfin tuwa ba, duk da kiraye-kirayen da wasu bangarori ke yi na yin hakan, tun bayan da aka fara kai hare-haren ta'addanci a kasar.

Kimanin 'yan gudun hijira 600,000, galibi daga kasashen Somaliya da Habasha da Sudan ta Kudu da kuma Uganda ne ka zaune a kasar ta Kenya, kuma kashi 70 cikin 100 daga cikin su 'yan kasar Somaliya ne.

Yanzu dai gwamnatin Somaliya ta yi alkawarin samar da yanayin da ya dace na mayar da 'yan gudun hijirar kasar zuwa gida.(Ibrahim).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China