in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dubban 'yan Nigeriya dake gudun hijira sun tsere zuwa Kamaru
2015-03-04 10:49:44 cri

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD UNHCR ta fitar da rahoton dake nuna cewa, kusan 'yan Nigeriya 16,000 ne dake gudun hijira suka tsere zuwa yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru dake makwabtaka da su cikin karshen makon nan da ya wuce, dalilin bata kashin dake wanzuwa tsakanin 'yan mayakan Boko Haram da sojojin kasashen yankunan.

Mataimakin kakakin majalissar Vannina Maestracci, ta bayyana cewa, daga ranar Laraban nan, hukumar HCR za ta yi aiki da kasar Kamaru domin tsugunnar da wadannan mutane a sansanin 'yan gudun hijira dake Kousseri mai tazaran kilomita 90 daga kan iyakar kasashen biyu.

Madam Vannina Maestracci, a lokacin da take ganawa da manema labarai ta yi bayanin cewa, za'a kaurar da 'yan gudun hijiran bayan nan zuwa sansanin dake Minawao, saboda an yi la'akari da yanayin tsaro da kuma yiwuwar karin 'yan gudun hijirar.

Hukumomin kasar Kamaru sun samu yawaitar shigowar 'yan gudun hijira mai tsanani ta kan iyakokinta na yankin Makaria, Logone Birni da kuma Fotokol, da kuma kudancin tabkin Chadi, abin da ke jawo masu harin 'yan Boko Haram daga Nigeriya.

Matsalar 'yan gudun hijirar kuma tana kawo rashin daidaiton tattalin arziki a yankin, wadda rahotannin bayan nan na shirin samar da tsaron abinci na duniya, da kuma binciken kan yanayin na kasar Nijar a watan Nuwambar bara sun nuna cewa, kusan kashi 52.7 cikin 100 na magidantar da suka rasa muhallansu, sannan kashi 14 a cikin 100 na masu masaukin bakin su ko kuma kashi 38.7 a cikin 100 na fuskantar rashin tsaron abinci, kuma suna da bukatar taimakon abincin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China