A wannan mako na baya, mun lura da kwararar mutane kimanin dubu 7 da kuma wadannan makwanni biyu na baya kimanin mutane dubu 14 suka iso, lamarin da muke ganin wata matsala cikin wata matsalar, in ji madam Ann Encontre, jami'ar da ke kula da harkokin 'yan gudun hijira ta HCR game da Sudan ta Kudu.
Madam Ann ta kara da cewa yawancin 'yan kasar Sudan ta Kudu da suka bar kasarsu mata ne da yara kanana da suka gujewa tashe tashen hankali a cikin jihohin Haut-Nil da Unite, yankunan da ke da arzikin man fetur.
Sudan ta karbi 'yan Sudan ta Kudu fiye da dubu 157 da suka bar kasarsu da ke fama da riciki, kuma kungiyoyin MDD dake aiki a Sudan sun nuna damuwa a baya bayan nan kan rashin kudin gudanar da aiki domin biyan bukatun 'yan gudun hijira na Sudan ta Kudu.
Kasar Sudan ta Kudu dai ta samu 'yancin kanta a shekarar 2011, amma ta fada cikin rikici a cikin watan Disamban shekarar 2013 a yayin da yaki ya barke tsakanin dakarun dake goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da sojoji masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Riek Machar.
Rikicin yayi saurin rikidewa a wani yakin da ya shafi kasar baki daya, tashen tashen hankali suka koma rikicin kabilanci inda 'yan kabilar Dinka ta shugaban kasa ke yaki da kabilar Nuer ta Riek Machar.
Wadannan tashe tashen hankali sun hadasa mutuwar miliyoyin jama'ar Sudan ta Kudu, da tilastawa kimanin mutane miliyan 1,9 barin gidajensu. (Maman Ada)