in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a "bude zuciya" a gaban matsalolin 'yan gudun hijira
2015-06-21 13:23:47 cri
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi kira a ranar Asabar ga gamayyar kasa da kasa da ta tuna duniyar da take raba wa tare kana da "bude zuciya" gaban matsalolin 'yan gudun hijira a ko'ina cikin duniya.

Mista Ban ya yi wannan kira a yayin bikin ranar 'yan gudun hijira ta duniya, da aka yi bikinta a ranar Asabar. Sakatare janar MDD ya nuna cewa yakin da ake yi a Syria, da rikice rikice a Iraki, Ukraine, Sudan ta Kudu, Afrika ta Tsakiya, arewacin Najeriya da ma wasu 'yankunan kasar Pakistan, sun taimaka sosai wajen karuwa da gaggauta tilasta wa mutane kaura daga muhallinsu a duniya.

A cewar wasu alkaluma na MDD, a shekarar bara, mutane dubu 42 da dari biyar sun zama 'yan gudun hijira, masu neman mafakar siyasa ko masu kaura na kasa da kasa a kowace rana, adadin da ya karu har sau kashi hudu a cikin shekaru hudu kawai. Kana kuma adadin 'yan gudun hijirar da suka koma gidajensu a shekarar bara ya kasance adadi mafi karanci tun fiye da shekaru talatin da suka gabata.

A cikin lokuta irin wadannan, yana da muhimmanci gwamnatoci da kungiyoyin fararen hula a duniya sun kara rubunya kokari wajen samar da matsugunni da kuma tsaro ga wadanda suka rasa kome a cikin yake yake ko kuma gallazawa, in ji mista Ban.

Babban taron MDD ya rattaba hannu kan wani kuduri a ranar 4 ga watan Disamban shekarar 2000, na maida ranar 20 ga watan Junin kowace shekara a matsayin ranar 'yan gudun hijira ta duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China