Ranar 20 ga watan Yuni rana ce ta 'yan gudun hijira ta kasa da kasa. A cikin sanarwarsa, Mr. Guterres ya ce, bayan da dan Adam ya samu wayin kai, taimakawa mutane marasa karfi kuma marasa galihu ya zama abin wajibi. Ko da yake akwai bambancin ra'ayi da ya kasance kan wasu batutuwa, amma kare wadanda suka yi gudun yaki ko suka gudu daga gidajensu sabo da ana gallaza masu wani nauyi ne da ya zama tilas na jin kai na kasa da kasa. Amma yanzu wasu kasashe masu arziki suna kalubalantar wannan ka'idar da ta dade tana kasancewa a cikin al'ummomi masu wayin kai, a idanunasu, 'yan gudun hijira suna kasancewa tamkar 'yan ratsa cikin gida, ko wadanda suke kwace guraban aikin yi, har ma ana daukar su masu ta'addanci. A gaban matsalolin 'yan gudun hijira, ko su dauki mataki ba a cikin yakini ba, ko su yi maganar banza kawai. Wannan rashin da'a ne, kuma karamin hange ne, da ma kuma ke tattare da hadari, in ji Guterres.
Mr. Guterres ya jaddada cewa, ya kamata kasashen duniya su sake karanta "yarjejeniya game da matsayin 'yan gudun hijira" da aka zartas a shekarar 1951, ta yadda za su iya cika alkawarin da suka dauka na bunkasa da kuma wadata duniyarmu baki daya. (Sanusi Chen)