Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan cikin wata wasikar da ya aike ga babban taron tattaunawa na wakilan bangarorin biyu da ya gudana jiya Asabar a nan birnin Beijing, ya ce ya dace bangarorin 2 su dukufa wajen musayar ra'ayoyi game da batutuwan da ke iya bunkasa rayuwar jama'un su, musamman a fannonin ilmi da kimiyya, al'adu, da yada labaru. Sauran fannonin sun hada da na inganta rayuwar matasa da mata, bangarorin da a cewar shugaban kasar ta Sin su ne ginshikan habaka dangantakar EU da kasar ta Sin.
A daya bangaren kuma shugaba Xi ya bayyana alakar dake tsakanin kasarsa da EU a matsayin daya daga cikin manyan huldodin ci gaba a duk fadin duniya, yana mai cewa taruka irin wadannan za su taimaka matuka wajen habaka ci gaban sassan biyu, wajen samar da dauwamammen yanayin zaman lafiya da ci gaba, da damar gudanar da gyare- gyare tare da wayewar kai.
Manyan baki a wajen taron na wannan karo dai sun hada jagororinsa, wato mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, da kuma kwamishinan sashen Ilimi, al'adu yaruka da inganata rayuwar matasa na EU Androulla Vassiliuo. (Saminu Alhassan)