in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da na EU sun aike wa juna sakwannin taya murnar cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakaninsu
2015-05-06 10:12:15 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban majalisar zartaswar ta nahiyar Turai Donald Tusk, da shugaban kwamitin kungiyar kasashen Turai EU Jean-Claude Juncker, su aike wa juna sakwannin taya murnar cika shekaru 40, da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin bangarorin Sin da kungiyar EU.

Shugaba Xi ya aike da sakwannin na shi ne a jiya Talata, inda ya bayyana cewa, Sin na dora muhimmanci kwarai ga alakar dake tsakanin ta da EU, kuma tana fatan ci gaba da kokari tare da shugabannin kungiyar EU, wajen amfani da wannan dama ta cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin sassan biyu, domin tashi tsaye, wajen kafa dangantakar abokantaka a wasu fannoni 4, duka dai a wani mataki na bunkasa dangantakar abokantaka, ta cimma moriyar juna, da samun nasara tare a dukkan fannoni.

A nasa sakon, Mr. Tusk cewa ya yi yana fatan dangantakar bangarorin 2 wadda ta shafi kasashe daban daban na Turai da kasar Sin, za ta bi hanyar ta samun ci gaba, domin daga martabar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin EU da Sin zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, Mr. Juncker ya ce yana sa ran kokartawa tare da kasar Sin, wajen sa kaimi ga samar da zaman lafiya, da wadata, da samun dauwamammen ci gaba, don kawo alheri ga kasashen Turai da Sin, da ma duk duniya baki daya.

A kuma dai wannan rana, firaministan kasar Sin Li Keqiang shi ma da wadannan shugabannin EU, sun aike wa juna sakwanni na taya murnar cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China