Shugaban Sin da firaministan Australia sun taya juna murnar daddale yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci
A yau Laraba 17 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaministan kasar Australia Tony Abbott, suka mikawa juna sakon taya murna, game da rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tsakanin kasashen biyu a hukunce.
Ana dai sa ran yarjejeniyar za ta ba da gudummawa wajen raya tattalin arziki, da cinikayya a yankin Asiya da tekun Pasifik, tare da sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin sassan biyu. (Fatima)