Rahotannin baya-bayan nan na cewa, jirgin yana dauke ne da mutane 458, ciki har da fasinjoji 406. Ya zuwa yanzu, gwamnatocin wurare dake gabobin tekun Yangtse na ci gaba da kokarin ceton mutanen da ke da sauran numfashi.
Bayan aukuwar lamarin, kwamitin tsakiya da majalisar gudanarwar Sin sun dora muhimmanci sosai game da wannan hadari da ya faru, inda shugaban Sin ya umarci majalisar gudanarwa da ta tura rukunin aiki don ceton mutane, kuma yana sa ran lardin Hubei da birnin Chongqing da sauran sassan da abun ya shafa za su yi iyakacin kokari don ceton mutanen da ke cikin jirgin, da shawo kan matsalolin da za su biyo baya. A sa'i daya kuma, ya ce, ya kamata a koyi darasi daga wannan lamari, don inganta tsaron muhimman ababen more rayuwa, don tabbatar da zaman rayuwar al'umma.
Shi ma firaministan Sin Li Keqiang ya bukaci ma'aikatar sufuri da ta dauki kwararan matakai don ceton mutane cikin gaggawa. A sa'i daya kuma, a yi kokarin ceton mutanen da ke cikin jirgin. Bisa bincike da hukumar kula da hanyoyin jiragen ruwa ta birnin Wuhan ta samu, an ce, an gano wurin da jirgin ruwan ya nutse, kuma zurfin wurin ya kai mita 15, ya zuwa yanzu, ana kokarin ceton mutanen da suka tsallake rijiya da baya.
A wata sabuwa kuma, an ce, da sanyin safiyar yau ne, ayarin 'yan sandan tsaron lafiyar jama'a na lardin Hubei ya dauki sojoji sama da 1000 da jiragen ruwa masu sauri 40 zuwa wurin da hadarin ya auku, don ceton mutane tare da killace wurin. Kazalika ma'aikatar sufuri da hukumar kula da yawon shakatawa ta Sin sun kaddamar da shirin ko-ta-kwana, sannan sun kafa rukunin aiki don daidaita lamarin.
Rahotanni daga cibiyar ba da umurni game da hadarin nutsewar jirgin ruwan, na cewa, rukunin ceton mutane na kokarin gudanar da ayyuka. Ya zuwa yanzu, an ce, an gano mutane 11, kuma 10 daga cikinsu na raye.(Bako)