Shugaba Xi yayi wannan kiran ne a yau jumma'a lokacin taro karo na 13 na kungiyar jagoranci na tsakiya akan ayyukan zurfafa kwaskwarima gaba daya, wanda aka kafa a watan Decemer shekara ta 2013 domin tafiyar da ayyukan kwakwarimar kai tsaye.
A lokacin taron shugaba Xi ya jaddada muhimmancin gwaje-gwajen da ake gudanarwa. Ya ce akwai bukatar kara kokarin ganin cewa wadannan gwaje-gwaje an tafiyar da su yadda ya kamata, wanda shi ne mabudin da zai sa sauran kwaskwarimar baki daya ya samu makoma mai kyau.
A wajen taron kungiyar ta amince da tsarin da aka fitar akan kwaskwarimar na kamfanonin mallakar kasa da bangaren shari'a.