in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Australia ta shirya maye gurbi idan har aka karbe damar karbar bakuncin kofin duniya na 2022 daga hannun Qatar
2015-06-12 09:15:39 cri
Kasar Australia ta bayyana aniyar ta ta karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2022, idan har aka karbe wannan dama daga kasar Qatar sakamakon tashin-tashinar cin hanci da rashawa dake girgiza hukumar FIFA.

Yanzu haka dai wasu manyan jami'an hukumar ta FIFA sun gurfana gaban kuliya, bisa zargin su da ake yi da aikata almundahana, matakin da ya sanya shugaban hukumar Sepp Blatter yin murabus daga mukamin sa. A daya hannun kuma, manazarta hankokin wasan kwallon kafa na ganin mai yiwuwa wannan hali da hukumar ya FIFA ta shiga, ya iya shafar makomar ikon da aka baiwa Qatar na karbar bakuncin gasar ta 2022.

Wani babban jami'i a hukumar wasannin kasar ta Australia John Eren, ya ce sun shirya tsaf domin karbar bakuncin gasar, ganin da ma a baya Australian ta nemi waccan dama da Qatar ta samu.

Qaatar dai ta doke Australia, da Amurka, a neman karbar bakuncin gasar ta 2022.

A cewar Eren 'yan gyare-gyare kawai za a yiwa wasu filayen wasan dake kasar, domin cimma nasarar karbar gasar ba tare da wata matsala ba, don haka a cewar sa babu wani gagarumin kalubale da kasar za ta fuskanta idan har aka bata damar karbar bakuncin gasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China