in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sauke Lobagnon daga mukamin ministan wasannin kasar Cote d'Ivoire
2015-05-21 10:34:12 cri

An sauke Lobagnon daga mukamin ministan wasannin kasar Cote d'Ivoire

Gwamnatin Cote d'Ivoire ta sanar a sauke ministan wasannin kasar Alain Michel Lobognon daga mukamin sa, bayan samun sa da laifin almundahana, ta kin biyan 'yan wasan kwallon kafar da suka wakilci kasar a gasar cin kofin duniya da ta gabata.

Shugaban kasar ta Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ne ya bada umurnin sauke Lobognon. An ce yawan kudin da ake batu, wadanda 'yan wasan kungiyar suka samu a yayin gasar a karon da ya gabata sun kai kimanin dala miliyan 1.27.

A ranar 9 ga watan Fabarairun da ya gabata, kungiyar kwallon kafa ta kasar Cote d'Ivoire, ta doke kungiyar kasar Ghana a wasan karshe na cin kofin kasashen Afirka na bana, wanda aka gudanar a kasar Equatorial Guinea, inda ta kuma lashe gasar.

Didier Drogba ya samu lambar yabo ta Barclays a fannin makasudin wasanni

A kwanakin baya ne mashahurin dan kwallon kafar kasar Cote d'Ivoire Didier Drogba, ya samu lambar yabo ta Barclays, a fannin taka rawar cimma nasarar makasudin wasannin motsa jiki, ciki hadda irin tarin gudummawa da ya bayar ga sha'anin jin kai a shekaru da dama da suka gabata.

Drogba dai na da asusu a nahiyar Afirka, wanda ke taimakawa matasan nahiyar masu sha'awar kwallon kafa. Sau da dama wannan asusu ya sha samar da kudi, da kayayyakin wasa ga kananan yaran nahiyar, wadanda ke makarantu domin samun horo da ilimi. Kana asusun ya yi kokari sosai wajen samar da gudummawa ga aikin kiwon lafiya.

Drogba ya bayyana cewa, an haife shi cikin iyali matalauta, kuma shi da abokansa su kan buga kwallon kafa a kan titi a lokacin kuruciyar sa, lamarin da ya samar musu da farin ciki kwarai. Ya ce a duk lokacin da ya ga yara su na murmushi yayin da suke taka leda, ya kan ji dadi. Don haka ne ma yake fatan taimakawa mutane, wajen samar da damar cimma burinsu a fannoni da dama. Ya kuma yi fatan al'ummar duniya za su rayu cikin koshin lafiyar jiki, da jin dadin rayuwa a ko wane lokaci. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China