in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaushe kasar Sin za ta nemi karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa?
2015-03-04 09:52:37 cri
A baya kasar Sin ta karbi bakuncin manyan gasanni na wasannin motsa jiki daban daban, cikin har da wasannin Olympics da aka gudanar a birnin Beijing a shekarar 2008, amma har ya zuwa yanzu ba ta samu damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na wasan kwallon kafa ba tukuna.

Amma ganin yadda kasar take da masu sha'awar wasan kwallon kafa fiye da miliyan 100, ciki har ma da shugaban kasar mista Xi Jinping, hakan ya sa ake sa ran ganin kasar ta yi sha'awar karbar bakuncin gagarumar gasar kwallon kafa ta duniya a nan gaba.

Sai dai a daya hannun Sinawa ba su da ra'ayi guda game da lokacin da ya dace kasar ta bayyana wannan buri na ta ga duniya ba.

A shekarar 2010, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin na lokacin, mista Wei Di, ya taba ba da shawarar cewa, kamata ya yi kasar Sin ta nemi karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026, sai dai sauran jami'an gwamnatin kasar ba su amince da wannan shawara sosai ba.

Amma a baya bayan nan, hukumar kasar mai kula da gyare-gyare, wadda ke karkashin jagorancin shugaban kasa Xi jinping, ta zartas da wani shiri na gudanar da manyan gyare-gyare ga tsarin wasan kwallon kafa na kasar Sin. Wannan labari ya sa an fara sake tabo maganar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya sosai.

A bangarensa, wani jami'i mai kula da wasan kwallon kafa mai suna Ding Changbao, wanda ya taba raka shugaba Xi Jinping na kasar Sin zuwa kasar Jamus, inda shugaban ya kalli wani wasan kwallon kafa da aka buga tsakanin matasan kasashen Jamus da Sin, ya ce sabuwar manufar da kasar Sin ta dauka a kokarin raya harkar wasan kwallon kafa a gida, mai yiwuwa ta taimakawa kasar cimma burita na karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.

Shi kuwa shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta lardin Jilin na kasar Sin, Song Jixin,cewa ya yi yana da imanin kasar Sin za ta ci gajiya a fannoni daban daban, ta hanyar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya. Ya ce, baya ga samun kudin shiga, karbar bakuncin wannan gasa zai taimakawa raya harkar wasan kwallon kafa a nan kasar Sin.

Wani shehu malami mai binciken al'adu masu alaka da kwallon kafa na kasar Sin, Jin Shan, shi ma ya bayyana ra'ayin da ya dace da na mista Song, inda ya ce kasashen Japan, da Koriya ta Kudu, sun zama abin koyi ga kasar Sin, ganin yadda kasashen 2 suka samu ci gaba sosai a fannin wasan kwallon kafa, bayan da suka yi hadin gwiwa wajen karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2002.

Sai dai yayin da masana da jami'ai masu kula da wasan kwallon kafa ke bayyana ra'ayoyin su game da kasar Sin, don gane da aniyar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya, wasu Sinawan na bayyana dari-dari ga wannan kuduri, ganin yadda kungiyar kwallon kafar kasar ke da rauni a fagen kware, wanda suke ganin hakan zai sanya ta fuskantar matsala.

Wani mai sha'awar wasan kwallon kafa ya ce bisa la'akari da yanayin da kungiyar kasar Sin take ciki yanzu, tabbas za a fid da ita a matakin rukuni, ko da ta shiga zagayen karshe na gasar cin kofin duniyar a matsayin mai masaukin bakin gasar. Don haka, a ganin sa babu bambancin shirya gasar da ba a yi haka ba.

Amma a nasa bangare, babban kocin kungiyar wasan kwallon kafa ta Guo'an ta birnin Beijing, mista Gregorio Manzano, yana ganin cewa kamata ya yi kasar Sin, ta bayyana niyyar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ba tare da wani bata lokaci ba, domin idan kasar ta samu wannan dama, hakan zai matukar sa ta kyautata yanayin da take ciki a fannin wasan kwallon kafa.

Shi kuwa wani koci da ya taba jagorantar kuloblikan Malloca da Atletico Madrid na kasar Spainiya, ra'ayin sa game da wannan batu shi ne, kamata ya yi a kau da kai daga tunanin sakamakon da kulaf din Sin ka iya samu, domin a cewar sa kasar Spainiya ta taba karbar bakuncin gasar a shekarar 1982, amma ba ta lashe kofin ba, sai dai wannan dama ta ba da ikon kyautata tsarin ta na gudanar da gasar kwallon kafa a cikin gida, tare da horar da 'yan wasan kasar bisa damar shirya wannan gasa.

A tarihin kungiyar kwallon kafan kasar Sin, karo daya ne kadai ta taba shiga zagayen karshe na gasar cin kofin duniya, wato a shekarar 2002. Sai dai a lokacin kungiyar ta tsaya ne a matakin gasar rukuni, inda ko kwallo daya ma ba ta ci.

A nashi bangare, shugaban kasar Sin mista Xi Jinping, a matsayin sa na mai sha'awar wasan kwallon kafa, bai gamsu da rawar da kungiyar kasar ta taka a baya ba, wanda hakan ya sa shi bayyana burin sa a wannan fanni dangane da kasar ta Sin a shekarar 2011, inda ya ce yana fatan ganin kungiyar kasar za ta sake shiga gasar cin kofin duniya a nan gaba, sa'an nan kasarsa za ta samu damar karbar bakuncin gasar, baya ga na karshe, wato kungiyar ta samu damar lashe kofin wata rana.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China