Figo ya ce hukumar FIFA za ta iya kara tsara shirye-shirye, wadanda za su sa kaimi ga bunkasuwar wasan kwallon kafa a nahiyar Afirka. Figo ya kara da cewa ana samun ci gaba, a fannin wasan kwallon kafa a nahiyar Afirka, amma ana fuskantar wasu matsaloli kamar na kudin da hukumomin kwallon kafar kasashen nahiyar ke samu daga gasannin kasa da kasa, da ma shirin raya wasan na tamaula. Kaza lika, yawan guraben da kungiyoyin kwallon kafar kasashen Afirka suke da su, a gasar cin kofin duniya, shi ma batu ne da ya dace a yi duba a kan sa.
Har wa yau, Figo ya yi fatan shugabannin hukumomin kwallon kafa na kasa da kasa dake nahiyar Afirka, ba za su nuna damuwa, game da canjin da za a samu a nan gaba ba, domin sauye-sauyen da ake da fatan aiwatarwa za su sa kaimi ga bunkasar kwallon kafa a Afirka, da ma dukkanin duniya baki daya. Figo ya ce, shi da jama'ar kasashen Afirka, masu matukar kaunar wasan kwallon kafa ne.
Baya ga Figo, sauran 'yan takarar dake neman shugabancin hukumar FIFA sun hada da shugaban ta na yanzu Joseph Blatter, da Prince Ali bin Al-Hussein na kasar Jordan, da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Netherland. Za a gudanar da zaben shugabancin hukumar ne dai a ranar 29 ga watan Mayun nan, inda mambobin hukumar 209 za su jefa kuri'u, ciki hadda 54 daga nahiyar Afirka.(Zainab)