Duk dai da cewa akwai sauran wasa guda a kammala gasar, tuni ta tabbata cewa Barca ta lashe kofin na bana, duba da cewa ta riga ta yiwa Real Madrid wadda ke matsayi na biyu tazara a yawan maki.
Barca ta buga wasan ne ba tare da dan wasan ta Luis Suarez ba, sakamakon raunin da ya samu. Duk da hakan Rodriguez ya taka leda yadda ya kamata, tare da sauran 'yan wasan kungiyar da ake gani a matsayin ajin farko wajen kwarewa. A daya hannun kuma Atletico Madrid ta fidda na ta kwararrun 'yan wasa, da suka hada da Antoine Griezmann, da kuma Fernando Torres wanda ya jagorance su.
Tun dai a farkon wasan Barca ta samu damammaki na cin kwallaye, amma hakan ya faskara, har sai cikin minti na 65 Messi ya zura kwallon da ta raba gardamar wasan. Bayan hakan Barca ta sha matsin lamba gabanin kammalar wasan, kafin a kai ga karshen wasan Barca na da kwallo daya Atletico Madrid na nema.
Ko ma dai yaya wasan da Real Madrid za ta buga zai kaya, hakan ba zai yi tasiri ga nasarar da Barcan ta samu ba, ko da yake hakan na iya nuna irin kwazon da 'yan wasan na Madrid suke nunawa, a wannan gaba da gasar ta La Ligar bana ke daf da kammala. (Saminu Alhassan)