Shugaban kulaf din Florentino Perez ne ya bayyana hakan ga taron manema labaru da ya gudana a filin wasa na Santiago Bernabeu, jim kadan bayan kammala taron hukumar daraktocin kulaf din.
Ancelotti dai ya bar Madrid a gabar da wasu ke ganin kakar wasanni ta bana ba ta yiwa kungiyar kyau ba. A dai wannan shekara Real Madrid ce ta biyu a gasar La Liga ta Sifaniya, inda take biyewa Barcelona. Kaza lika Atletico Madrid ta doke ta a wasan karshe na cin kofin King's Cup. Har wa yau Juventus ta doke ta a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun turai.
Da yake karin haske game da sallamar kocin na Madrid, Perez ya ce kulaf din na bukatar manyan nasarori, kuma yanzu lokaci ya yi da za a kara azama wajen bunkasa karfin kungiyar. Ya ce za a bayyana wanda zai maye gurbin Ancelotti nan da mako mai zuwa.
Ancelotti dan asalin kasar Italiya, ya fara horas da Real Madrid da kafar dama, bayan da ya jagoranci kungiyar ta dauki kofin zakarun turai a karo na 10 a tarihinta, ta kuma dauki kofin King's bayan ta doke Barcelona a wasan karshe.
Sai dai duk da irin wadannan nasarori da ya samu, an yi hasashen raba gari tsakanin Ancelotti da Madrid tun lokacin da aka cire kulaf din daga gasar cin kofin zakarun Turai na bana, duk kuwa da cewa wasu daga 'yan wasan kungiyar kamar su Cristiano Ronaldo, sun bayyana kaunar su ga ci gaba da kasancewar kocin a kulaf din.
Kafin Real Madrid Ancelotti ya horas da manyan kulaflikan duniya kamar Valencia, da Liverpool. Akwai rade-radin cewa mai yiwuwa a nada kocin Napoli Rafa Bentiez, a matsayin sabon kocin Real Madrid.(Saminu Alhassan)