in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin hanci da rashawa a hukumar FIFA
2015-06-04 09:27:17 cri

Jaridar "The Economist" ta kasar Birtaniya ta bayyana cewa, ana samun aukuwar laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa matuka, a fannin wasannin matsa jiki, wadanda hukumomin kasashe daban daban ke jagoranta. Karkashin shirin neman ikon karbar bakuncin gasanni, cikin sirri wasu jami'ai ko kungiyoyi ke matukar arzuta kan su.

Kaza lika jaridar ta ce cikin kungiyoyin wasanni da suka fi aikata zamba, wadda ta fi tafka almundahana ita ce hukumar wasan kwallon kafa ta FIFA. Jaridar "The Economist", ta ce a matsayin ta na babbar hukumar duniya mai kula da fannin wasan kwallon kafa, wadda kuma babu mai sanya ido a kanta, ta yi kaurin suna wajen aikata zamba.

Magabacin Joseph Blatter, kuma tsohon shugaban hukumar FIFA, Mista Jean Havelange, ya fara jagorantar hukumar a shekarar 1974. A cewarsa, hukumar FIFA tana da dalar Amurka 20 kacal a asusun ajiyarta a lokacin. Domin samun kudin da ake bukata na gudanarwar hukumar, Havelange ya yi kokarin alakanta wasan kwallon kafa da cinikayya, lamarin kuwa da ya haddasa yaduwar cin hanci da rashawa a hukumar.

A nasa bangare, shahararren dan jaridar BBC Andrew Jennings, ya kwashe shekaru 5, yana bin diddigin yanayin wasan kwallon kafa a kasashe 18, tare da wallafa wani littafin wanda ya tona asirin hukumar FIFA game da cin hanci da rashawa, da aikata magudi a zabe, da dai makamantansu. Game da wannan littafi na Andrew, bari mu dubi wasu daga tabargazar da ake zargin hukumar ta FIFA da aikatawa a cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata.

Da farko dai Jean Havelange, tsohon shugaban hukumar FIFA, wanda ya kasance mai mallakar wani babban kamfanin sufuri a kasar Brazil, bayan zama shugaban FIFA ya yi kokarin tallafawa kamfanin ISL mai samar da kayayyakin wasanni. Mun san FIFA tana da hulda mai kyau da kamfanin ADIDAS, ta yadda dukkanin kwallayen kafa da ake amfani da su a gasar cin kofin duniya kamfanin ADIDAS ne ya samar da su. Kuma sanin kowa ne kamfanin ISL tsohon shugaban kamfanin ADIDAS Hoster Dassler ne ya kafa shi. Kamfanin da a cewar Andrew Jennings, ya yi matukar ba da cin hanci ga manyan kusoshin kungiyoyin wasanni sosai.

Ya ce hukumar FIFA ita ma ta ci moriya sosai daga wannan kamfani. An ce bayan da Havelange ya yi ritaya a shekarar 1998, kudin da FIFA ta ajiye a banki ya kai dala miliyan 400.

Koda yake wadannan kudi da hukumar FIFA ta tara ba a tabbatar da cewa ko ta taru su ne ta haramtacciyar hanya ko akasanin haka ba, a daya hannun akwai laifin da ake ganin yiwuwar tabbatar sa. Ga misali a shekarar 2010, shi Andrew Jennings ya zargi shugabannin hukumomin wasan kwallon kafa na latin Amurka, da na Brazil, gami da mataimakin shugaban hukumar FIFA da cin hanci da rashawa, inda ya gabatar da wasu takardun sirri na kamfanin ISL, a matsayin shaidu ga yadda shugabannin suka karbi rashawa tsakanin shekarun 1989 zuwa 1999.

Bayan da Joseph Blatter ya hau kujerar shugabancin hukumar FIFA a shekarar 1998, an rika samun karin aikata almundahana. Ga misali, an ce kafin Blatter ya samu zama shugaban FIFA, akwai wasu boyayyun abubuwa da ya yi wadanda suka ba shi taimako, ciki hadda ba da kudi masu yawa ga 'yan majalisar hukumar FIFA. Har ma aka ce akwai dan majalisar da ya samu dalar Amurka dubu 50 daga wajen shi Blatter. Ban da haka kuma, zuwa shekarar 2010, don kare mukaminsa a babban zaben hukumar ta FIFA, Blatter ya ware dala biliyan 1 don kula da hulda da dukkan wakilan kasashe mambobin hukumar su 208.

Zuwa shekarar 2014, jaridar "The Thames" ta kasar Birtaniya, ta fidda wasu takardun sirri, wadanda ke nuni da yadda albashin manyan kusohin hukumar FIFA ya ninka, inda matsakaicin albashin ya kai dalar Amurka dubu 200. Ban da haka kuma, shi kan sa shugaban FIFA Blatter, ya cire kimanin dala miliyan 5, daga ribar da FIFA ta samu a gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Afirka ta Kudu, inda ya yi amfani da kudin a matsayin kudin bonas da aka baiwa jami'an hukumar FIFA. A nan an ga yadda ake kokarin tona asirin hukumar FIFA, sai dai duk da haka, ba a samu damar hana hukumar ci gaba da hakan ba.

Sa'an nan an fi samun aukuwar abubuwan kunya a manyan gasannin cin kofin duniya da zasu gudana tsakanin shekarun 2018 zuwa 2022. Ga misali, kafofin watsa labaru na kasar Argentina sun ba da labarin cewa, bisa burin neman samun damar karbar bakuncin manyan gasannin, hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Qatar ta taba ware makudan kudi da ya kai dala miliyan 78.4 don sayen kuri'un goyon baya daga Marigayi Julio Grondona, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Argentina a lokacin, kuma tsohon mataimakin shugaban hukumar FIFA, wanda ke kula da harkar kudi a hukumar. Lamarin wanda a cewar jaridar the Thames ya sa Grondona ya goyi bayan kasar Qatar, don haka a karshe kasar ta samu biyan bukatar ta.

Ban da haka kuma, jaridar ta "The Thames" ta ce yayin da kasar Rasha ke neman karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2018, firaministan kasar na lokacin Vladimir Putin ya taba kokarin lallashin Mr. Blatter, tare da ba da kyauta ga sauran manyan kusohin hukumar.

A wannan karo kuma, ma'aikatar shari'a da hukumar 'yan sanda ta FBI dake kasar Amurka, sun tona yadda jami'an FIFA suka aikata laifukan cin hanci da rashawa. An ce bisa kokarin da ake yi na shirin gudanar gasar "Copa Amurka" a kasar Amurka a shekarar 2016. Karo na farko kuma da za a gudanar da gasar a wajen latin Amurka a tarihi, wasu jami'an FIFA da na hukumomin wasan kwallon kafa na kasashen Latin Amurka sun yi matukar karbar rashawa, kudaden da ake ganin sun kai dala miliyan 110.

Amma abun mamaki shi ne yadda hukumar FIFA ta kaucewa fuskantar shari'a, duk da cewa an gabatar da shaidu da yawa don tabbatar da cin hanci da rashawa da jami'an ta ke aikatawa. Kuma ya zuwa yanzu kalilan ne daga cikin jami'an ta aka gurfanar gaban kotu. Haka kuma hukumar ta yi wa mutumin da ya yi karar ta, wato Mr. Andrew Jennings bita-da-kulli, inda ta yi kokarin kakaba masa takunkumi.

Dalilin da ya sa haka kuwa shi ne, kasancewar an kafa hukumar a kasar Switzerland, kasar da ta yi suna wajen kasancewa 'yar ba ruwanmu. Saboda haka, hukumar ta kasance ba ta da wasu masu kula da ita, kana babu wata kungiya dake da ikon sa ido kan ayyukan hukumar.

Bisa wannan muhallin da take ciki ne, hukumar ta tsara wasu ka'idojin da za su amfani jami'an ta. Ga misali, ta kayyade cewa idan an samu laifi a cikin hukumar, bai kamata a kai kara ga wata kotu ba, maimakon haka, ya kamata a bari kwamitin musamman na ladabtarwar hukumar ya dauki matakan da suka dace. Lamarin da ya sa ake ganin yadda hukumar ke ci gaba da kokarin kare matsayin ta game da zarge-zargen da ake yi mata.

Yanzu haka dai FIFA ta dade tana gudanar da harkokinta yadda ta ga dama, tamkar babu wanda zai iya girgiza tsarinta. Sai dai kamar yadda ake cewa, "ba kullum ake kwana a gado ba", wani lokaci ma sai dai a kwana a kasa. Don haka, matakan da a yanzu karin kasashe, da jama'arsu suka fara mai da hankali game da batun cin hanci a hukumar ta FIFA, mai yiwuwa ne a kai ga shawo kan matsalar da ta dabaibaye hukumar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China