Madam Hua Chunying ta bayyana hakan ne a yayin wani taron menama labaru da aka shirya a yau Jumma'a, inda ta ce, mahukuntan kasar Sin na mai da hankali kwarai ga bunkasa huldar dake tsakanin kasar da kasar Najeriya.
Ta ce, bana shekara ce ta cika shekaru 10 da kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, kuma bangaren Sin yana fatan hadin kan Najeriya, ta yadda sassan biyu za su kokarta tare wajen karfafa zumuncin gargajiya, da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, ta yadda za a iya kara ciyar da huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu zuwa matsayi na gaba. (Sanusi Chen)