in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya Liberia murnar kawo karshen yaduwar Ebola
2015-05-25 20:36:50 cri
Kwanan baya ne, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar da kawo karshen yaduwar cutar Ebola a kasar Liberia, kana shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ta mika sako ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, domin nuna godiya kan babbar gudummawar da kasar Sin ta baiwa kasar wajen yaki da cutar Ebola.

A nasa bangaren, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga shugaba Sirleaf, inda ya bayyana cewa, kasar Sin aminiyar abokiyar kasar Liberia ce, don haka ya kamata Sin ta dauki alhakin taimaka wa kasashen Afirka dake fama da cutar Ebola wajen yaki da cutar.

A halin yanzu kuma, bisa jagorancin shugaba Sirleaf, gwamnati da jama'ar kasar Liberia sun yi nasarar yaki da cutar Ebola,har aka kawo karshen yaduwarta a duk fadin kasar, dangane da haka, gwamnati da jama'ar kasar Sin sun taya kasar murna da kuma yabo matuka kan wannan nasara.

Bugu da kari, kasar Sin na son taimaka wa kasar Liberia kan yadda za a farfado da tattalin arziki da yanayin zaman takewar al'umma, bayan da aka kawo karshen yaduwar cutar Ebola a kasar, haka kuma, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban, domin tallafawa jama'ar kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China