in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta fitar da Laberiya daga jerin kasashe masu fama da Ebola
2015-05-09 20:55:59 cri
Hukumar lafiya ta dauniya WHO ta ce yanzu haka kasar Laberiya ta samu kubuta daga mummunar cutar nan ta Ebola, bayan da aka kwashe kwanaki 42, ba tare da samun wani ya kamu da cutar a kasar ba.

Yayin kwarya-kwaryar bikin murnar cimma wannan nasara da aka gudanar a Asabar din nan a asibitin John F. Kennedy, shugabar kasar Ellen Johnson-Sirleaf, ta yi godiya ga ubangiji, bisa tallafin da ya baiwa kasar ta, ta yadda al'ummar ta suka kubuta daga wannan cuta.

Shugaba Sirleaf ta kuma ziyarci asibitocin kasar da dama, domin tabbatarwa al'ummar ta cewa an kawo karshen Ebola a kasar. Ta kuma godewa jama'ar kasar, bisa juriyar da suka nuna yayin mawuyacin hali da suka shiga a baya.

Game da yanayin da ake ciki a kasashen Guinea da Saliyo kuwa, shugaba Sirleaf ta ce suma kasashen biyu dake makwaftaka da kasar ta, na daf da kaiwa ga matsayin kawo karshen cutar a yankunan su.

WHO dai ta bukaci da a yi taka-tsan-tsan, har ya zuwa lokacin da za a kai ga dakile cutar daga sauran kasashen biyu.

Cutar Ebola ta hallaka mutane sama da 11,000 tsakanin kasashe uku na yammacin Afirka inda ta fi tsananta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China