in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin likitocin Sin a Liberia ya dawo gida
2015-05-17 16:50:57 cri
Likitoci 42 da Sin ta tura zuwa kasar Liberia, domin ba da taimako ga 'yan kasar sun sauka a nan birnin Beijing cikin koshin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an lafiyar sun iso gida ne da sanyin safiyar Lahadin nan, bayan kammala aikin shawo kan cututtuka, da ba da jiyya na tsawon watanni biyu.

An labarta cewa, wannan ne rukuni na uku da Sin ta tura zuwa kasar Liberia. Kuma jami'an rukunin sun yi kokarin matuka, wajen gudanar da aikin jiyya, da kyautata kwarewar likitocin kasar, da taimakawa gwamnatin Liberia wajen kyautata yanayin rayuwa, da na kiwon lafiya, sun kuma ba da taimakon jin kai yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China